Sabon Labari:Tinubu Yana Koyi Da Muhammadu Buhari

Hot Posts

Install Truenigeriamini On Your Phone
6/recent/ticker-posts

Sabon Labari:Tinubu Yana Koyi Da Muhammadu Buhari


Sabon Labari:Tinubu Yana Koyi Da Muhammadu Buhari

Babban Dan Takarar Jam'iyyar SDP Ya Bayar da Ra'ayinsa Kan Wasu Kura Kure Da Tinubu Keyi Irin Na Buhari 


Lauyan da ke  a Najeriya kuma dan takarar a zaben shugaban kasa daga jam'iyyar SDP, Prince Adewole Adebayo, ya bayyana damuwarsa game da hali da tattalin arzikin Najeriya yake ciki. 

Ya ce tinubu yana koyan wasu bakaken manufofi. Cikin wata hira da Adewole ya yi, yayin da yake nazarin mummunar kura kuran da Tinubu yake yi a cikin watanni uku da ya jagoranta.


A ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, Adewole Adebayo, wanda ya fito takara a matsayin shugaban kasa daga jam'iyyar SDP, ya ce Tinubu yana yana bin wasu hanyoyi na samar da tsaro iri daya da Muhammadu Buhari da yayi, wanda kuma hakan beyi aiki ba

Ya bayyana haka a lokacin da yake yin murna kan watanni uku da shugaban kasa ya yi a mukamin. Yana nazarin yadda tattalin arzikin Najeriya ya ragu a lokacin da Tinubu ke jagorantar.


A wani rahoto da Daily Trust ta wallafa, Adewole ya nuna cewa ba daidai bane yadda ake yin tallafi a kasashen duniya. “A Amurka, suna tallafawa kan magunguna, da kiwon lafiya; a Burtaniya, tallafinsu ya shiga cikin sufuri.”


Adewole ya bayyana babu kwaraiwa a yadda shugaban kasa ya cire tallafin. Ya kira ga Tinubu ya gyara kuskurensa.

Post a Comment

0 Comments